Mallam ina wuni ina da tambaya, tunda nayi aure da mijina yau shekara daya matsala muke tasamu ,iyaye sun shiga cikin maganan suna san su raba auren shi kuma miji bayaso , meye hukuncin in ni na ce inasan koma wa mijina sukuma iyaye sun nace sai an raba auren.
Matsalar auren, mijina miskili ne ba mai san magana bane kuma baida hayaniya nikuma shirunsa nake sa wa naga kaman bai sona, har na gaya maa iyayena su kuma suna ganin kaman bai sona shi yasa suke san araba auren nikuma mallam bana san araba ..
AMSA
*******
Gaskiya babban laifin yana wajenki. bai kamata ki rika daukar Sirrin mijinki kina gaya ma iyayenki ba. Musamman tunda ba wani cin mutuncinki yake yi ba, kumq bqi rage miki komai daga cikin hakkinki akansa ba.
Ke da kanki kin bada shaidar cewa mijinki mutum ne mai shuru-shuru bai cika son magana ba. Kin ga kin zalunceshi kuma kin zalunci kanki..
Abinda ya kamata kiyi shine ki sameshi ki bashi hakuri ki nuna masa kuskurenki. sannan ki samu iyayenki ta hanyar da ta dace. Ki gaya musu cewa kin gaya musu laifinsa ne don suyi masa nasiha ba wai don su raba auren ba.
Idan ba zaki iya gaya musu gaba da gaba ba, ki nemi wani yayanki ko kawunki ki shaidar masa. shi kuma yaje ya sanar dasu.
Igiyar aure kuwa tana hannun mijinki. idan ba shi ne yace ya sakeki ba, kina nan amatsayin matarsa.
Allah ya sawwake.
Dan wannan nake jan hankalin matan aure cewa ku guji daukar maganganu kuna gaya ma iyayenku. Ku dena gaya musu sirrin mijinku. wannan ba daidai bane. domin kiyaye sirri yana daga cikin alamomin Mace tagari.
WALLAHU A'ALAM.