1. Akwai wani aikin lada wanda dukkan musulmai sun yarda dashi.. Yara basu yi sosai.. Manya sun fi yi.. Dariya yakan 'bata wannan aikin. Amma kuka yana gyarashi..
2. Shin tsakanin sallah da azumu wannene yafi girma?? Na san zaku ce SALLAH!!
To mai yasa mata masu haila suke ramukon Azumi amma basu yin ramukon sallah??
3. Akwai wasu birane guda biyu (Ba Makka bane, ba Madinah bane) amma mafiya yawan Manyan Annabawa da Manzanni sun ta'ba ziyartarsu ko zama cikinsu.... Wadanne birane ne???.
4. Akwai wasu Mataye guda uku. Su ba Annabawa bane, amma sunyi zance da Mala'iku. Kuma labarinsu yazo acikin ALQUR'ANI..
Shin wadanne Mata ne?
5. Akwai wadansu Qwari guda uku wadanda Allah ya buga misali dasu acikin ALQUR'ANI mai girma... Amma kowanne daga cikinsu yana iya chutar da 'Dan Adam...
Na farkonsu zallarsa chutarwa yake yi. Na biyu kuma Amfaninsa yafi chutarsa yawa.. Kuma ba zai cuceka ba, amma idan ka chuceshi sai ya rama.
Na ukunsu kuma, zai zo ya cuceka, amma idan ka rikeshi zai baka maganin chutar..
Shin wadanne Qwari ne?? Kuma acikin wadanne surori Allah ya fadi labarinsu??