Idan Ajalin Mumini yayi, Mala'ikun Rahama zasu zo su Karbi ruhinsa, Sannan su tafi da ruhin izuwa Sama ta bakwai.
Achan ne sauran Rayukan Muminai (wadanda suka sanshi aduniya) zasu zo su kewayeshi suna tambayarsa labarin duniya.
Mala'iku zasu ce musu "KU KYALESHI YA HUTA TUKUNNA.. KUN SAN BAI JIMA DA BARIN GIDAN WAHALA BA (DUNIYA").
Bayan ya huta Zasu tambayeshi labarin iyalansu da 'yan uwansu.. Shi kuma yana gaggaya musu.
Idan suka tambayeshi labarin wani, zai ce musu ai ya rigani rasuwa. Shin bai zo muku ba?.
Zasu ce bai zo nan ba. Watakil an tafi dashi chan wajen Uwarsa HAWIYAH, ACIKIN QASA TA-BAKWAI. Hawiya ita ce Mummunar Uwa.".
(Ibnul Jawzee ya kawo hadisai da yawa masu irin wannan ma'anar acikin littafinsa mai suna AHWALUL QUBOOR).
YA ALLAH KA KIYASHE MU SHARRIN HAWIYA. YA ALLAH KASA MUNA CIKIN BAYINKA SALIHAI DON RAHAMARKA.