Assalamu Alaikum Dafatan Malam Yana Lfy, Allah Ya Kara Girma Da Lapia Ameen. Malam Nayi Tambaya Ta BBM Sati Daya Kenan Amma Har Yanzu Shiru Ba'a Amsa Min Ba Ko Wrong Pin Nake Dashi Wanine Yake Amfani Da Sunan Zauren Fiqhu A Matsayin Account Dinsa ? Shirun Da Naji Shine Yasa NaTuro Su Ta Email. Malam Tambayoyi ne Dani Guda Uku Gasu Kamar Haka
1. Ta Daya Mutum Ne Yana Azumi Na Ramadan Sai Sha'awa Ta Kamashi Har Ya Zamana Yai Releasing Maniyyi Yafita Bata Hanyar Saduwa Ba Ya Azuminsa Na Wannan Ranar Yake??
2. Sai Tambaya Ta Biyu Amaryace Da Ango Sukai Sabon Aure Kafin Azumi Sai Ya Zamana Idan Angon Ya Dawo Gida Amaryar Tana Rungumarsa Har Suyi Releasing Ya Azumin Su Yake ?
3. Tamabaya Ta Uku Kuma Ya Ya kamata Ai Ciyarwar Azumin Kaffara Za'a Iya Rabawa Biyu Ko Lokaci Daya Za'ai Gaba Daya? Ina Bukatar A Boye Id Na, Bissalam, Allah Bada Ikon Amsawa Ameen.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh. Ameeen Allah shi amsa Addu'ar da kayi mun.
Hakika ba wrong pin bane. domin ina da pin guda biyu wadanda nake amfani dasu a BBM. kuma kowanne an rubuta ZAUREN FIQHU ajikinsa.
Kuma naga Wadannan tambayoyin naka. sai dai yawan uzurarruka ne yasa ban samu damar amsa maka ba.
1. Tambayarka ta farko da ta biyu duk amsarsu guda ce. Idan mai azumi ya fitar da maniyyi ta wata hanyar da ba ta jima'i ba, Misali ta hanyar shafa, ko kallo, ka rungumar juna, to Azuminsa ya karye, kuma zai rama guda daya ne rak.
Amma idan yayi jima'i da rana acikin watan Azumi, to sai ya rama azumin wannan ranar tare da kaffarar Azumi guda sittin. Idan ba zai iya ba, to sai ya ciyar da miskinai sittin.
2. Ciyarwar da ake yi amatsayin kaffara, bayarwa gaba daya lokaci guda yafi alkhairi gareka tunda zakayi ne amatsayin Horo (Punishment). Sai dai in babu damar yin hakan sai ka raba gida biyun.
Kuma zaka bayar da gwargwadon abincin da miskinai sittin zasu ci su Qoshi ne.
Ya kamata matasa mu rika girmama alfarmar watan na ramadhan mai girma. Mu guji aikata duk abinda zai kawo mana lalacewar azuminmu ko zubewar ladansa.
WALLAHU A'ALAM.