TAMBAYA TA 1579
*******************
Assalama alaikum da fatan Mallam yana lafia. Allah ya kara wa Mallam ilimi da baiwa da bashi ikon fahintar da mutane akan addinin Allah ameen.
inada tambaya menene hukuncin mai alwala kuma sai ya kalli tsaraici kamar iyalansa ko nashi ko na yara kanana?
kuma menene hukuncin iyayen da suke haramtawa yayansu da su auri kabila kaza da kaza harma idan ka tambaye su mai yasa basu da hujja mai karfi wanda zasu baka. Daga ADAMU IBRAHIM USMAN.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Hukuncinsa shine alwalarsa tana nan. sai dai idan wannan kallon tsaraicin ya haifar masa da fitar Maziyyi to alwalarsa ta karye.
Hukuncin iyayen da suke haramta ma 'Ya'yansu auren wata Qabila, wannan abinda suke yi ba daidai bane. Domin kuwa shi Musulunci addini ne wanda ya daidaita tsakanin dukkan mabiyansa koda launin jikinsu ko yarensu yasha bamban.
Babu wata Qabila wacce tafi wata Qabila awajen Allah. Kuma babu fifiko tsakanin fararen fata da Bakake. Sai dai mafi tsoron Allah, Shi ne yafi girma awajen Allah din.
Bai halatta mutane su rika kirkirar Hukunci ba.. Domin kuwa duk wanda ya haramta abinda Allah ya halatta, to ya kafirta. kamar yadda kuma duk wanda ya halatta ma kansa abinda Allah ya haramta, to ya kafirta.
Iyaye masu irin wannan halin ya zama wajibi suji tsoron Allah su dena.
WALLAHU A'ALAM.