Daga cikin dubban abubuwan da kafiran turawan nan suka kawo ma duniya, babu abu mafi hadari, mafi saurin hallakarwa kamar DEMOCRACY (Siyasar Demokradiyya).
Na san mutane da yawa zasuyi mamakin jin wannan kaoamin daga gareni. Amma haka batun yake. kuma duk wanda ya san wani abu game da addini, idan ya nutsa sosai cikin karatun Siyasa zai tabbatar da dukkan abinda nake fada.
Ita dai siyasa Abu ne mai dauke da hannaye guda uku daban daban masu alaka da juna.
Hannu na farko shine Bangaren shari'a: yana Qunshe da kotuna da alkalai da lauyoyi da sauransu.
Wannan bangaren shi keda alhalin yin Shari'a atsakanin jama'a da jama'a ko kuma tsakanin Gwamnati da jama'a.
HANNU NA BIYU : shine bangaren Majalisa yana kunshecda Majalisun tarayya da na Dattijai. Shi keda alhakin tsara dokoki tare da bada shawara ga bangaren Shari'a da na zartarwa.
HANNU NA UKU : Bangaren Mulki da zartarwa. Shi keda alhakin tabbatarwa da zartar da abubuwan da Kotuna ko Majalisu suka miko.
To babban hadarin abun anan shine: Daga cikin wadannan bangarorin guda uku babu wani bangaren da ya dauki Littafin Allah da Sunnar Manzonsa (saww) amatsayin babban Kundin da za'a rika dauko kowacce irin doka daga cikinsa.
Hasali ma fassarar ma'anar Demokradiyya shine MULKIN JAMA'A DAGA JAMA'A. Wato jama'a ne zasu zabi shugabansu, da kuma wakilansu.
Su wakilan ne zasu zauna su tsara dokokin da suka dace da raayinsu, sannan su mika ma gwamnati ita kuma ta zartar.
Alhali mu kuma abisa dokokin addininmu na Musulunci, dukkan Doka da Mulki da gudanarwa gaba daya na Allah ne shi kadai.
Da wannan nake so in ja hankalin 'Yan uwa Musulmai cewa Ku dena daukar Demokradiyya amatsayin wani Mikakken tsari wanda Allah yake so. Sannan ku dena kafirta junanku ko cin mutuncin juna saboda ra'ayin da ba zai fissheku alahira ba.
ZAUREN FIQHU.