Fudhail bn 'Iyaad daya ne daga cikin Magabata na kwarai.
Yace na koyi hakuri da juriya ne daga wajen wani Qaramin yaro.
Watarana na fito zan tafi Masallaci sai naga wani yaro mahaifiyarsa ta dokeshi yana ta kuka, har ta koroshi waje, ta rufe kofar gidan.
Na wuce na tafi naje nayi sallah. Amma har na dawo na tarar da yaron nan ya dena kukan ya dawo ya zauna akofar gidan mahaifiyarsa yana jiranta ta bude masa kofa.
Chan sai naga ta bude kofar gidan, yaron yazo ya shiga, Uwar ta tarairayeshi cikin tausayi da soyayya irin na mahaifiya..
Da ganin haka sai na fashe da kuka har sai da gemuna ya jike da hawaye........
Ina tunanin cewa: Da ace mu 'yan Adam muna iya daurewa mu zauna akan Qofar Ubangijinmu kamar yadda yaron nan yayi hakuri ya zauna akofar gidan mahaifiyarsa, to da tabbas Ubangiji zai jikanmu ya bude mana kofofin rahamarsa. Domin kuwa soyayyar da Ubangijinmu yake yi mana tafi soyayyar da wannan Uwar take yiwa 'danta...
ZAUREN FIQHU :