Wacce ta shayar da Manzon Allah (saww) ita ma ta ga abubuwan mamaki daga albarkar Wannan Shugaba (saww).
Tunda ta daukeshi ta fara shayar dashi ta fara ganin albarkacinsa. Jikinta ya samu lafiya daga chutar yunwar dake tare da ita, Hakanan dabbar da take kai ita ma ta samu kuzari fiye da irin na sauran dabbobi.
Kuma tunda ta kaishi gidanta shikenan ta rabu da talauci ko Quncin rayuwa saboda albarkacinsa. Tumakinta da awakinta sunyi albarka sosai. Sun haifu fiye da yadda sukeyi ada. Sannan kuma albarkar nononsu ya Qaru.
Da kanta take cewa bata ta'ba ganin mutum mai albarka irin wannan yaron da take shayarwa ba!!
ASSALAMU ALAIKA YA KHEERATALLAH (SAWW)