TAMBAYA TA 1584
===============
Assalamu Alaikum da fatan Malam yana cikin koshin lapia Malam ina da tambaya Kamar haka.
1.ya halatta na ziyarci kabarin mahaifina (baba na) ?
2. Wace irin Addu'a yafi dacewa nake yiwa BABA na ?
Allah yasa mu dace Amiiin
Daga Umar Isawa
AMSA
*******
Eh ya halatta ka ziyarci Qabarinsa kamar yadda yazo acikin hadisi, Manzon Allah (saww) ya kasance yana ziyartar Makabartar Baki'a. Kuma yana yiwa mamatan cikinta addu'a.
Sayyidah A'isha watarana ta tambayi Manzon Allah (saww) daga ina yake? Sai yace mata yaje Makabartar Baqee'ah ne.
Hadisin yana nan acikin Bukhariy kuma Muslim ya kawoshi akan lambar hadisi na 976.
Awani hadisin kuma yace "KU ZIYARCI QABURBURA, DOMIN ZATA TUNASAR DAKU LAHIRA".
- Muslim hadisi na 974.
Addu'ar da zaka yawaita yo masa ita ce "Allahummaghfir Li'abee warham-hu. Wa'afu anhu wa aafihee. Allahumma wassi'i madkhalahu wa nawwir lahu feehi.
Ma'ana: Ya Allah ka gafarta ma Mahaifina kaji Qansa. Kai afuwa agareshi, ka kiyayeshi daga fitinar lahira.
Ya Allah ka yalwata makwancinsa, kuma ka haskaka masa acikinsa.
Kuma ya halatta ka karanta wani abu daga cikin Alqur'ani dominsa. Misali kamar Suratul Ikhlaas.
Kuma kar ka manta da Addu'ar shiga makabarta irin wacce Manzon Allah (saww) yake yi yayin shigarsa Baqee'ah.
Kuma ka kiyaye kar ka aikata wani abinda Allah ya haramta, kuma kar ka shagaltu da daukar hotuna, ko kuma wani abu marar amfani idan kaje wajen.
Wallahu a'alam.