Muhammad Ibnul Hanafiyyah (rah) ya ruwaito daga Mahaifinsa Imam Aliyyu bn Abi Talib (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"ZANYI TA YIN CETO ARANAR ALKIYAMA HAR SAI ALLAH MADAUKAKIN SARKI YACE MIN "SHIN WANNAN YA ISHEKA YA MUHAMMADU?".
NI KUMA ZAN CE "EH YA ISHENI YA RABBI".
Acikin wani hadisin kuma yace : "CETONA ARANAR ALKIYAMA GASKIYA NE. DUK WANDA BAI YI IMANI DA ITA BA, TO BA ZAI ZAMANTO DAGA MA'ABOTANTA BA"
- Ibnu Katheer ya kawo hadisin acikin AN-NIHAYAH FIL FITAN WAL MALAHIM.
Ya Allah sanya dukkan daliban ZAUREN FIQHU acikin sahun gaba na ceton Manzon Allah (saww). Kuma ka sanyamu cikin masu yin ceto ga sauran Muminai. ka sanya iyayenmu da iyalanmu baki daya.