Annabi Dawud da Taalutu sun fita filin yaki tare da Sojoji 313 sun Gwabza yaki da wasu Dubunnan Sadaukai (Giants) irin su JAALUT. Amma su sukayi nasara duk da cewa an fisu yawa, an fisu Qarfi..
Annabi Musa (as) ya fito tare da mutanensa talakawa marassa arziki ko kayan yaki.. Fir'auna kuma ya fito da dukkan Qarfinsa na Dakarun sojoji da Mugayen Makamai.. Amma duk da haka Allah ya bama Annabi Musa (as) nasara, ya hallakar da Fir'auna da Mutanensa.
Arabar yakin badar, Annabinmu MUHAMMADU (saww) ya fita tare da Sahabbansa guda 313, babu isashen guzuri ko kayan yaki..
Su kuma kafirai sun fito da fiye da mutum dubu daga cikin Jarumansu da manyan garinsu. ga kuma tanadin miyagun Makamai da sukayi, Amma Allah ya bama Annabi Muhammadu (saww) nasara tare da Sahabbansa.. kuma ya kunyatar da kafiran Quraishu ya Qaskantar dasu..
Ya Allah kamar yadda kayi ma wadannan Annabawan naka, Ya Allah don kadaitakar Zatinka, da Dawwamar Mulkinka, da tsarkin Siffofinka, Ya Allah ka bama Musulunci nasara akan kafirci, ka Cetomu daga mawuyacin halin da muke ciki, ka chanza mana Azzaluman Shugabanni ka bamu wadanda zasu kwatanta adalci akanmu.