Daga Sayyiduna Aufu bn Malik (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"MALA'IKA JIBREELU yazo min daga wajen Ubangijina, cewa in za'ba tsakanin abubuwa guda biyu:
1. Ko dai Rabin al'ummata su shiga Aljannah.
2. Ko kuma a bani ceto (Mai Girma).
Sai na za'bi cheton. Kuma ina son duk wanda yake wajen nan ya zama shaida cewar duk wanda ya mutum ba ya hada Allah da wani wajen Bauta, to zai samu shiga cetona.".
Baihaqiy ne ya ruwaito daga Auf bn Malik Al-ashja'iy (ra).
Ya Allah ka kiyaye mana imaninmu, mu rayu dashu, mu mutu dashi don hasken Alqur'aninka.
DAGA ZAUREN FIQHU.