Akwai wata fitsara wacce ta dade tana damun mafiya yawan mutane masu mu'amala da Social Media kamar irin su Whatsapp da facebook.
Wannan fitsarar ita ce yadda zaka ga matan aure (harma wadanda basu taba yin auren ba) suna yin dogon rubutu wai suna koya ma junansu yadda ake yin Jima'i!!! harma akwai Audio recording da muryar wata fitsararriyar mata marar kunya wai tana koya ma mata yadda zasu rika kwanciya da mazajensu!!!
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!!! Kwanakin baya ZAUREN FIQHU yaci karo da irin wadannan rubutattukan nasu... Amma mamaki da takaici ya hana inyi magana!!!
Wannan wacce irin ba'dala ce!!! Wannan wacce irin fitsara ce!!! Yanzu masu yin wannan suna da amsar da zasu bama Allah aranar da zasu tsaya agabansa???!
Shin waye yazo ya koya ma iyayensu mata yadda zasuyi Jima'i da nasu Mazajen har aka samu ciki aka haifesu!!
Illolin da wannan abu yake haifarwa acikin al'ummah suna da yawa.. bq zasu lissafu ba...
Akwai Qananan yara maza da mata wadanda ta dalilin sauraro ko karanta wadannan abubuwan suka afka cikin ZINA da makamantansu.
Koda irin wannan zai yi amfani, to cutarwarsa tafi amfaninsa yawa. Allah ya shiryi masu yi.
ZAUREN FIQHU