Daga cikin Qazaman Al'adun turawa wadanda Wasu mutane suke koyi dasu, babu mafi Qazanta da kuma hadari fiye da irin abubuwan da matasa sukeyi wai don nuna murnarsu akan Qaruwar aure da suka samu.
Tun Kafin aure zaka ga Matasa suna rungumar juna suna daukar hotuna suna nuna ma duniya cewa su fa basu jin Kunyar Allah ma ballantana bayinsa.
FITSARANCI NA BIYU : Shine Bikin Party da ake yi. Za'a tara abokan ango da Qawayen amarya, Sannan arika sanya Kidan disko, su rika fitowa suna Tikar rawa!! Ana shaye shayen kayan Maye, Wiskey, Weewi, Kwayoyi,da sauransu.
Daga karshe za'a kira angon ya fito tare da Amaryar, su fito suna RAWA A BAINAR JAMA'A!!! DON TSABAR RASHIN KUNYA, DA KUMA BUTULCI GA UBANGIJI!!
3. FITSARANCI NA UKU : Shine Mother's Day. wato ranar bikin uwar amarya. Ita ma zata tara dattijai da sauran "Kasaitattun mata" irinta Suyi rawa su gwangwaje.
Ubangiji ya amsa rokonku, ya cika muku burinku, Amma maimakon kuyi masa godiya, sai kuka zabi ku tara jama'a ku aikata sabonsa, Domin nuna masa cewa KU FAJIRAI NE!!
Gaskiya Wallahi ba don Tausayi da jin kai na Ubangiji ba, da nan take an kifar da garin ma baki daya!!
Yanzu kwanan nan akwai wani Video Clips da suke yawo ta na'urar WHATSAPP. wasu ango da amarya ne suke tikar rawa agaban jama'a, ana eehu ana fitsaranci!!
- Yanzu shin masu irin wannan auren, idan sun haifi Fitsararrun yara, menene abin mamaki aciki??
- Yanzu ba zaku ji kunyar Watarana iyayenku, ko kuma 'ya'yan da zaku haifa zasu ga wannan abinda kuka aikata ba??
- Yanzu ba zaku rika tuna tsayawarku agaban Ubangiji ba, ranar da zai tambayeku akan kowacce ni'imar da yayi muku!!
Wannan Tunatarwa ce. Wanda yaga dama ya wa'azantu, ya amfani kansa. Wanda ya gani kuma yayi biris dashi, to ya cuci kansa.
DAGA ZAUREN FIQHU.