Manzon Allah (saww) yace "Yayin da Mutum ya rasu, 'yan uwansa suna kokarin shirya jana'izarsa, wani kyakyawan Mutum zai zo ya tsaya akansa.
Yayin da aka sanya masa likkafani, wannan kyakyawan mutumin zai zo ya shiga tsakanin likkafanin da kuma Qirjin mamacin.
Bayan an binneshi 'yan uwansa sun koma gida, shi wannan kyakyawan zai ci gaba da zama tare dashi har zuwa lokacin da wasu Mala'iku guda biyu (Munkar wa Nakeer) zasu shiga Qabarin suyi kokarin raba tsakanin mamacin da kuma wannan kyakyawan mutumin domin su samu damar yi masa tambaya akan addininsa.
Wannan kyakyawan mutumin zai ce musu "Wannan mutumin fa abokina ne, kuma Sahibina ne. Don haka ba zan iya rabuwa dashi ba. Idan an turoku kuyi masa tambaya ne, to kuyi masa tambayar amma ni dai ina nan tare dashi, ba zan barshi ba har sai na shigar dashi Aljannah.
Sannan zai juya wajen Mamacin yace masa "Nine Alqur'anin da ka kasance kana karantawa aduniya, wani lokacin afili, wani lokacin kuma aboye. Kar ka damu. Bayan wadannan tambayoyin da Munkar da Nakeer zasuyi maka, babu sauran wani bakin ciki agareka".
Bayan Wadannan tambayoyin sun Qare, wannan kyakyawan Mutumin zai shiryo masa kyakyawar Shimfida tun daga Mala'ul A'ala.
(Ibnul Jawzee ya tattaro irin wadannan hadisan acikin Littafinsa mai suna AHWAALUL QUBOOR)