1. Mutanen Alqur'ani sune Mutanen Allah – in ji Manzo (saww).
2. Allah zai 'daga darajojinka aduniya da lahira.
3. Alqur'ani zai zama Hujjah agareka aranar Lahira.
4. Idan ka karanta Alqur'ani ka sauke wani nauyin da Allah ya 'dora maka.
5. Allah zai jefa kwarjikinka acikin Zukatan halittunsa.
6. Yayin da kake tsakiyar karanta Alqur'ani, rahamar ALLAH zata lullubeka.
7. Mala'ikun Allah suna halartar wajen da kake karatun.
8. ALQUR'ANI zai zama abokin hirarka cikin Qabarinka. kuma shi zai haskaka maka shi. Kuma zai debe maka kewa.
9. Aranar Alkiyama Allah zai tasheka acikin manyan Mala'ikunsa masu daraja..
10. Akwai lada goma da Allah zai baka akan kowanne harafi guda daga cikin harrufan Alqur'anin da kake karantawa. Misali Basmalah tana da harrufa 19. kuma ladan karanta Basmalah ya zama 19x10 = 190.
11. Alqur'ani zai zo ya ceceka agaban Allah. ba zai bari akaika wuta ba.
12. Zaka shiga cikin inuwar Allah aranar da babu wata inuwar sai ita.. kana tare da Annabawa da zababbun Allah.
13. Idan ka tsufa, ba zaka samu rikicewar Kwakwalwa ba. Kuma ba zaka dimauce yayim mutuwarka ba.
14. Malamanka da iyayenka zasu rika samun lada kwatankwacin irin wanda ka samu yayin da kake karanta Alqur'ani.
15. Zaka samu daukakar daraja acikin gidan aljannah gwargwadon yawan ayoyin da ka haddace.
Ya Allah muna godiya agareka da ka sanyamu acikin Mahaddatan Littafin nan naka mai girma. Ya Allah ka azurtamu da yin aiki dashi yadda kake so. Ya Allah ka Qara mana tsantsar Taqawa sa Ikhlasi don falalarka da rahamarka.
ZAUREN FIQHU.