Annabin Allah Musa mutum ne mai jin kunya kuma yana suturta al'aurarsa babu mai ganin fatarsa saboda tsananin kunyarsa.
Al'adar Banu Isra'ila ba ta hana su yin wanka a kwabe waje guda ba kowa na ganin al'aurar kowa a fili. Annabi Musa kuma ya kasance duk lokacin da zai yi wanka, sai ya kebe wajen da babu mai ganinsa kafin ya kwabe kayansa ya shiga cikin gulbi don yin wanka.
Banu Isra'ila sai suka kasance suna gulmarsa har ma suke cewa: Ba komai yasa yake barin cikinmu ya kebe ba sai dai ko yana da kuturta ko kazuwa ko dai wata cuta a fatarsa da ba ya so mu gani.
Allah yai nufin ya barrantar da annabinsa daga wannan zargi. Wata rana annabi Musa ya kebe ya kwabe kayansa ya ajiye su a kan dutse ya shiga tafki yai wanka. Bayan ya gama sai ya fito ya nufi dutse don ya dauki kayansa. Kawai sai dutse ya gudu da kayan annabi Musa. Sai annabin Allah ya dauki sandarsa ya bi dutsen yana ce wa: Bani kayana.. Bani kayana... Dutse kuma ya ki tsayawa har sai da ya zo wajen jama'a daga cikin Banu Isra'ila sai ya tsaya.
Banu Isra'ila suka ga annabi Musa a kwabe suka ga babu wanda ya kai shi kyan fata sai suka ce: Allah ya tsine wa makaryata!
Annabi Musa ya karasa wajen dutse ya dauki kayansa ya sanyasu. Annabi Musa ya dauki sandarsa ya fara bugun dutsen har sau uku a gaban Banu Isra'ila dutse yana kuka kowa yana jin kukansa.
Haka Allah yake kubutar da annabawansa da mutane kirki daga duk wani sharri da aka yi musu.