1. Idan ya zamto baka jiran sallah sai dai sallar ta jiraka.
2. Idan ya zamto kwana biyu zuwa uku baka bude Qur'aninka ba.. (wai baka da lokaci).
3. Idan ya zamto ka fi damuwa da ka burge mutane, koda zaka sa'ba ma Ubangijinka.
4. Idan ya zamto kullum tunanninka yadda zakayi ka tara Kudi da dukiya.. Baka tuna wahalar hisabin da zaka sha idan dukiyar ta taru.
5. Idan ya zamto baka da aiki sai musu ko jayayya duk lokacin da wani yayi maka nasiha akan abinda kake aikatawa bai dace ba.
6. Idan ya zamto kana jinkirta ayyukan alkhairi irin su kyauta, sadaqah, zumunci, sai gobe.. Sai jibi... Etc.
7. Idan ya zamto da zarar kaji labarin fitowar wata sabuwar waya ko receiver, burinka shine ka Mallaketa ko ta halin Qaka!!
8. Idan ya zamto babu rayuwar da take burgeka sai irin ta Mawaka da 'yan Drama da 'yan kwallo, da masu dukiya.
9. Idan ya zamto kai da abokanka kullum sai gasar chanza riguna da hawan motoci.
10. Idan ya zamto Qananan ayyukan zunubi bassu damunka ballantana manyan.
11. Idan ya zamto kana jinkirta tuba alhali baka san lokacin da mutuwa zata riskeka ba.
12. Idan ya zamto baka da Kishirwar samun ilimin gyaran addininka. Sai dai na gyaran duniyarka. (BOKO).
13. Idan ya zamto zaka shafe rana guda bakayi tunanin mutuwarka da kwanciyar Qabarinka ba.
14. Idan ya zamto kana iya zuwa ka saba ma Allah ta hanyar Zina, cin kudin ruwa, da sauransu. duk da ka san cewa abun babu kyau.