بسم الله الرحمن الرحيم
وصلى الله على محمد وآله وصحبه وسلم
Kishi wani abune mai kyau idan aka saka shi a wurin daya dace, yakan zama mummuna idan ya zarce yadda ake buqatarsa, kamar yadda ake sarrafa dawa akeyin kamu da ita asha, idan aka jiqata kwanakin suka wuce sai ta zama giya, ko ruwan kwakwa da yake zama bammi da sauransu.
kishin maza zaizo a wajen Miji na Qwarai bayan nagama da Matata Gari.
Mace tagari takan nisanci mummunan kishi domin yakan rage qaunarta a zuciyar mijin batare da ta saniba, wata matar takan yi kishi da uwar mijinta, wata har da 'ya'yan da ta haifama bawai 'ya'yan kishiya ko ita kanta kishiyar ba.
Irin wannan kishin yakan 6ata gidane gaba daya, ya 6ata rayuwar aure data maigidan da 'ya'yansa har da ita kanta matar.
A dan iya shekarun da nayi, naga matar data kashe kanta saboda kishi, wai bazata zauna da kishiya ba.
Naji wacce tanemi ran mijin Allah ya qwace shi.
Naga wacce tanemi sabautashi maqwabta suka kai masa dauki.
Sannan naji wace ta zubawa kishiyar da 'ya'yanta fetur zata saka wuta Allah ya qwacesu.
Naga wace ta saka aka kori mijin daga wurin aikinsa.
Naga wace take addu'ar Allah ya talautar da mijin don karya iya aure.
Wata tasa an kashe kishiyar.
Wata tanemi an haukatar da ita.
Wata tanemi sakin matar.
Wata ta sayar da lahirarta gaba daya don kawai wani dadi maras tushe a duniya.
kai ni naga wace ta saka 'ya'yan kishiyarta a gaba, bata qaunar jin alherinsu.
Wai dacewa duk wadannan suna ganin abin da sukeyi daidai ne.
Irin wannan yasa magabatanmu Allah yasaka musu da alkhairi maganarsu a ranar budar kai tafi qarfi wajen hana mummunan kishi.
Shiyasa Abdullahi bn Ja'afar (R.A) yayiwa 'yarsa nasiha a ranar kaita daki dacewa:
"Inayi miki kashedi da kishi domin mabudin saki ne.
Kul da yawan zargi don yakan kawo qiyayya.
Kisaba da tozali"
Kishi yakan wargaza gida ne.
Shiyasa yazama dole a wajen mace tagari ta nesance shi.
Macen data kamu da wannan cutar ta kishi zaka riske ta kullum a cikin tsoron cewa wata zatazo ta qwace mata shi.
Shin me wancan take dashi da ita bata dashi ???
Me wancan takeyi da ita bata iya ba, ko kuma bazata koya ba ???
Idan budurci ne shekara Daya tayi yawa zaku zama uwaye.
Idanma ke kin sanshi samada ita, kin gaje gidan da 'ya'yan farko, ashe itace zatayi kishi dake.
Meyasa kike kishi da ita ?
Haqiqa kishi ba qaunar miji bane, kawai shakka ne da tsoro na rashin mijin.
Wato galibi mata basu da sakankancewar zuciyar mijin a kansu, don haka zasu kadaita hankalinsa akansu koda arziqi koda tsiya.
Matan Annabawa da sahabbai sunyi kishi, amma nason ace mijin ya amfana dasune kawai, na neman yardar mijin ne a lahirance, kowa tana qaunar samun lada.
Shiyasa wata ta iya kyauta da kwananta, don ba shine matsalarta ba, aljanna take nema tareda manzon rahama, ko kin fahimci Hausata ???
Ku biyoni a darasi na 7 gobe.