بسم الله الرحمن الرحيم
وصلى الله على محمد وعلى آله وصحبه وسلم
Mace ta qwarai tasan irin maganar data kamata tayi da inda ya kamata tayi, da kalmomin da suka dace ta furta, ta kuma san matsayin mahaifinta a wurinta don haka ba wani abu bane mai wahala ta ajiye maigidanta a matsayinsa, wannan mahaifanta ne, sune komai nata na rayuwanta, haka wannan maiginta ne, shine komai nata na rayuwanta, ciyar da ita, shayar da ita, sha'awarta, tufafinta, matsaguninta da duk abin da suka shafi duniyarta da lahirarta.
Don haka idan tazo yin magana da maigidanta tasan irin yadda zata isar da saqonta, domin Ubangijinta daya sakata a qarqashinsa yana kallonta, zata iya zama dashi ta tattauna matsalarta dashi.
Wani lokaci ma takan kai harda jayayya idan yanemi liqa mata liqaqqiya amma kada ta daga masa murya, domin wannan ba sifar mumina bace.
Idan taga ya fusata ta rabu dashi, in har shedan yasa ta daga masa murya to tayi kukan yin hakan, tayi nadama ta kuma roqeshi ya yafe mata, ta canza halinta.
Mace tagari bata daga muryarta ga mijinta zaqi ne dashi kamar zuma, ga taushi sama da ruwa, ga dadin zance da kyawun hali.
Ta san yadda zata hana mijinta fita, da yadda zata dawo dashi gida ba magana ba komai.
Itace maigidanta zaiyi niyyar qaurace mata da tabude baki saita mantar da shi.
Wannan yasa Allah (S.W.T) yahana matan Annabi (S.A.W) yin amfani da muryarsu ta Biyu a Suratul Ahzaab.
Domin kar mai sha'awa yayi kwada yi!
Wannan muryar ado ce ga mace, shiyasa Allah ya bata bai ba namiji ba, mata suna da wannan makamin na yaqin zuciya amma kadan ne a cikinsu suka iya amfani da shi.
Domin ga yaqi yana cinsu kullum sunqi koyon yadda zasuyi amfani dashi.
Idan mace ta iya bakinta ta tsabtace gidanta da kanta da 'ya'yanta to dole kyawunta ya bayyanana koga mata bama mijinta kadai ba.
Mace mai tsabta tsufanta baya bayyana.
kyawunta kullum fitowa yakeyi, kuma tafi kowa sanin yadda zata janyo mijinta kusa batare da tayi asarar kalmomi ba.
Mace takan sami taimakon zuciya wajen karya lagwan namiji.
Shiyasa wata take cewa:
"Ina mamakin wautar macen da namiji yafi qarfinta alhali kuma yana yawo ne a tafin hannunta!"
Mace tagari takan yi darasin warware matsalarta ba tare da tashin hankali ba.
Kyawun jikinta dana maganarta dana muryarta da na dakinta, kicin dinta da ban dakinta, duk wasu abubuwa ne na siyan hankalin mijinta.
Ayyukan gida da wahalhalun da take sha wasu abubuwa ne dasuke fito da kyawunta sarari a idon mijinta da duk sauran masu kallonta.
Fushi da tashin hankali basa hanata tayi amfani da muryarta don cin ma burinta.
Wadannan sifofin mace ta qwarai kenan.
Sai mun hadu a darasi mai zuwa.