بسم الله الرحمن الرحيم
وصلى الله على محمد وآله وصحبه وسلم
A duk lokacin da na wayi gari naga matata tana matuqar qaunata tana girmamani, tana yimin biyayya daidai gwargwadonta, toba shakka bani da wata abokiyar rayuwa wace ta wuceta, itace abokiyar shawarata saboda amincinta, itace asusuna saboda amanarta.
Amma idan na wayi gari naga cewa ni kawai takeso ba ruwanta da iyayena da 'yan uwana, haqiqa komai nata zai fado qasa, haka zan dena ganin girmanta kamar yadda ta dauki iyayena, ba yadda za ayi na girmama nata, ni ta wulaqanta nawa, halin namijin qwarai kenan a jiya da yau.
Mace itace wace kullum take fatan ganin farin cikin maigidanta, daci gabansa, sabo da hakane 'yan uwansa suka sami albarkacinsa.
Mace ta qwarai tana son dangin mijinta yara da manya, takanyi musu kyakkyawan zato idan sukayi kuskure, takan taimaka musu daidai iyawarta, ta girmamasu, ta wadata su da abinci, da kyaututtuka, tariqa zuwa sha'anoninsu gaba daya na haihuwa dana mutuwa, ta dage sai taga maigidanta yana taimaka musu, wannan zaisa su soshi sosai, itama su saki jiki da ita, har ma idan suna neman wani abu sai kiga sun biyo ta hannunta.
Uwarsa kuma baza taji nauyin shiga gidansa ba, don tasan yana da mata ta qwarai.
'Yan uwansa duk zasu sota.
Da yawa zaka taras mace ta qwarai tana bawa mijinta shawara yayiwa 'yan uwansa da mahaifansa alkhairi, ya ziyarce su, ya tambaye su ko suna son wani abu, ba wace take korar 'yan uwansa tana kawo nata ba, tahana iyayensa ta kaiwa nata, taqi girmama iyayensa tace shi kawai take aure ba iyayensa ba.
Wannan shine sikelin da ake auna mata tagari da matar banza.
Wannan uwace, ta haifi da da cikinta tasha wahalar renonsa, ta qaunace shi, ta san komai na rayuwarsa da tsaraicinsa, wannan qaunar tana girma kamar yadda shima yakeyi.
Farat Daya sai zuciyarsa ta rabu da ita ta koma kanki, yadena cin abincinta sai naki.
Ya dena sirri da ita saike, hatta murmushinsa da ita ba kamar naki ba, yana yaro ne yake kwana da ita a gado daya, yanzu sai dai ke ki shigar dashi wani dakin kija qofa ki kulle.
Kenan kin qwace mata komai daga hannunta, ashe wannan bai isa kiyi mata hanzari ba idan tana cutar dake.
Idan kuma batayi ki saka mata da wahalhalunta ?
Haba 'yar uwa, Kiduba kigani, kin qwace komai daga hannunta da mijnta da sauran 'yan uwansa ya kamata kiyi tunani.
Duk namijin da yaga matarsa tana son iyayensa da 'yan uwansa yakan saki jiki da ita, kuma shima zai riqa kyautata wa mahaifanta, ya girmama su.
Idan kuwa ta wulaqanta iyayensa da 'yan uwansa tariqe nata, haqiqa ta janyo masa baqin jini daga 'yan uwansa.
Hatta maqwabta da sauran jama'a sun dunga zaginsa kenan.
To ina soyayyar asalin take ?
Aure ba gidan kasuwanci bane da za a riqa tunanin riba, aure wajen neman lahira ne ba duniya ba, wajen neman qaunar abokin rayuwa ne daci gabansa da daukakansa.
Sai mun hadu a darasi mai zuwa.