بسم الله الرحمن الرحيم
وصلى الله على محمد وآله وصحبه وسلم
Biyayya ga miji ba mai iyawa sai mace ta tagari.
Da yawa mata suna so ace sune wadanda Annabi (S.A.W) ya sifanta dinnan da (Nagari) saidai biyayyar itace tayi qaranci, ko za ayi saidai a gabansa, idan ya matsa an watsar kenan.
Wallahi na taso na taras ada iyayenmu mata magabata suna kwatantawa.
Furaat bn Sa'ib yake cewa Umar bn Abdil'Azeez yacewa matarsa lokacin daya ganta da wani jauhari da ubanta yabata.
"Ki za6i Daya cikin Biyu, kodai ki mayar dashi baitul mali ko kuwa kibani damar rabuwa dake!
"Tace"A kan mene ?
Nafi sonka sama da ninkokinsa"
Sai yasa aka mayar, yayin da yarasu dan uwanta Yazeed yahau karaga sai yace in tana so zai dawo mata dashi, sai tace:
"Wallahi sam!
Mijina ya hanani amfani dashi a lokacin da yana da rai sai bayan yarasu zan dawo dashi ?
"To mace kenan tagari a gidan miji na gari.
Asma'u bnt Kharijatul Furaziy take cewa 'yarta ranar budar kanta cewa:
"Yanzu fa kinfita daga sheqar da aka qyanqyashe ki zuwa shimfidar da baki santa ba, da abokin rayuwar da baki san shiba, ki zamar masa qasa sai yazamar miki sama, kizamar masa shimfida zai zama miki turaku, ki zamar masa baiwa, zai zama miki bawa, kar ki nace wajen neman abubuwa domin karya gujeki, kar kiyi nisa dashi domin karya manta dake, idan ya matso, ki kusance shi, idan yaja jiki, kema ki dan ja da baya, amma ki kiyaye hancinsa da kunnensa da idonsa, karya shinshini komai a wurinki sai qamshi, kar yaji komai sai kyakkyawan abu, kar yaga komai sai wanda zai burge shi.
Mace tagari takan yi qoqarin tazamar wa mijinta aljannarsa ce, batason taga gazawarta a idanunsa, don haka takan yi farin ciki idan taga murmushinsa, takan damu matuqa in taga fushinsa koda bada ita yake ba.
Bata jinkiri a wajen abinci, kuma ta iya dafawa batare da almubazzaranci ba, itace amintacciyar abokin shawararsa, mai iya riqe masa sirri, bata yarda wani yasani ko waye kuwa, sannan ga taimako.
Allah sarki!
Wani mutum yatashi tafiya hajji yana tunanin abin da zai barwa iyalinsa, sai matar tace karya damu ga masara can a gidan wane, buhu 12 ta saya.
Sai yayi mamakin inda ta samo kudin, tace masa, wanda yake bayarwa ne, in akayi aikin gida kudin yaragu sai ta 6oye saboda tunanin gaba, yau kusan shekara 7 kenan ko fiye, da faruwar hakan, gashi yau sunyi mana rana.
Allah kuwa matan wannan zamani kuna biyayya ga mazajenku na aure ?
Matsayinka na namiji idan kasami mace irin wannan wane yanayi zaka tsinci kanka ???
Sai mun hadu a darasi mai zuwa.