بسم الله الرحمن الرحيم
وصلى الله على محمد وآله وصحبه وسلم
Nayi wani nazari sai nagano iyayenmu na baya sun fimu sanin aure da matsayinsa, wannan yasa idan za a yiwa namiji aure murna da farin ciki yake dabaibaye shi, har ana buga misali cewa:
"Wace fara'a kakeyi haka kamar wanda yayi amarya ?
"Ita kuwa amaryar kuka takeyi tun kafin 'yan kwanakin ranar auren, saboda zullumin irin rabuwa da iyaye da kuma tarin aikace-aikacen da zasu hau kanta, yau sai muka sami kanmu angon zullumin sha'anin gida duk sai ya dabaibaye shi har kaji ana buga misali:
"Tunanin me kakeyi haka kamar wani mai mata ?
"Ita kuwa murna tacika ta harji take kamar takai kanta, duk wani party zaka ganta cikin fara'a, ita da kanta take raba katin gayyata.
Gaskiya akwai buqatar gyara, mace tagari aikinta Daya ne ga mijinta mai rassa da yawa, wato shigar da farin ciki a zuciyarsa ta duk hanyoyin da suka halasta, don haka bai yiwuwa a sami mace ta qwarai sai wace ta hada kyau na 6oye da na sarari, tabada rayuwarta ga Allah sannan hidimar mijinta, ita ba mijin take fara kallo ba, a'a, wanda ya sakata tabishi wato Allah (S.W.T).
Babban abin dake jawo qauna kyawun 6oye da na sarari.
Kyawun 6oye shi ne:
Tsoron Allah, girmama iyayen miji da daukansu a matsayin mijin.
Son 'yan uwansa, kunya, ibada da rashin rowa ga 'yan uwan miji, kyawun sarari kuwa:
Iya kwalliya, sa tozali, abin hannu, zobe da sutura mai kyau, lalle da turare kuwa suna da sirrorinsa na shigar da qauna da daga sha'awar miji da janyo hankalinsa da qarfi da matso dashi kusa, wannan yasa muslunci nan take yabayyana rufe qafa a sarari a maimakon fuskar da ake tsammanin ita ke fitar da kyawun mace, yahana mace saka turare tafita, har Annabi ya sifanta mai fesa turare tafita da MAZINACIYA!
Abin dazai baka mamaki, ba macen da tayi aure bata tsallake matakin budurci ba, da wani abu tariqa jan hankalin samari ?
Matanmu yau (wasu) sun dauki aure a matsayin qaddara kawai, suyi aikin gida, su haifi 'ya'ya, suyi raino, wannan yasa basa kwalliya sai dare, ko idan zasu fita,hatta yaransu qanana marasa hankali sun san kwalliyar fita waje, wata macen ma bata san qanshin turaren mata ba bare ta gaya maka, lalle kuwa kadan ne daga cikin mata suka san matsayinsa, in kaga sunyi to, akwai wani sha'ani, babbar sallah ko qarama, ko sauran bukukuwa, wadan da ba ruwansu da lallen mace.
Lalle domin sha'awa ake yinsa, kenan mutum Daya kacal ake masa, shin kinayi masa ko sai akwai sha'ani a gidanku ?
Mace Allah ya riga yayita kyakkyawa, sai in bata iya gyara kanta ba, duk lokacin da wani yaga muninta yarabu da ita, wani zai ga kyawunta ya dauka.
Allah (S.W.T) yariga ya qawata son mata a zuciyar maza, ko mijinki yana yaba adonki ko baya yi, ki tabbata yana jin dadin kallonki, ke ado ce, tauraruwa, farin wata sha kallo.
kiji tsoron Allah kisaka wannan baiwar da Allah yayi miki ga mijinki don farin cikinsa da kwanciyar hankalinki.
Sai mun hadu a darasi mai zuwa.