Malam don Allah a taimaka min, na Dan yi ciwon nono kwanaki har na Dena bawa yarona nono, toh yanzu ya warke amma ruwan nono ya dena zuwa, na Ga kwanaki kace a nemi nonon akuya da garin alkama, amma na kasa samun nonon akuya, akwai wani abun da zan iya sha ya dawo don yarona bai kai shekara ba. Allah Ya saka da alheri, nagode.
AMSA
*******
Eh akwai abinda zakiyi kamar haka:
Ki samu ingantancen garin hulba kullum ki rika dafa cokali guda da ruwa kofi guda. idan ya tafasa sai ki sauke ki sanya Zuma sosai aciki, sannan ki rika sha. Kiyi haka safe da yamma.
Idan kuma akwai man Hulba din, ki rika sha kina shafawa ajikin nonon. Zai Qara girma, kuma ruwan zai samu sosai. In sha Allah.
Kuma zai kashe kwayoyin chutar Cancer wadanda suke kawo ciwon nonon. Sannan zai magance miki ciwon Sanyi, ciwon Sugar, da sauransu.
Allah yasa a dace.
Wallahu a'alam.