1. Mafiya yawa sukan yi auren ne don kashe wutar sha'awarsu kadai.
2. Wasu kuma suna yi ne don burgewa saboda abokanansu sunyi.
3. Wasu kuma suna yi ne don cimma wasu bukatunsu na duniya, ko kudi ko mulki ko don Qulla dangantaka da wani Mashahurin mutum.
Wadanda suka ci riba mai yawa sune wadanda sukayi aure don cika umurnin Ubangiji, da kuma koyi da sunnar Muhammadur Rasulullahi (saww).