1. tana rage ma masu yinta Qarfin Imani.
2. Tana debe musu kunya.
3. Tana debe musu Amana da aminci.
4. Tana kore Tsoron Allah (Taqwa) daga zuciyoyin masu yinta.
5. Tana wanzar da talauci.
6. Tana wanzar da bakin ciki.
7. Masu yinta suna yin mummunan tsufa.
8. Tana wargaza zuriya.
9. Tana lalata zukatan zuriyar masu yinta.
10. Tana harba ma ruhi mummunar nar chuta.
11. Tana sanya munafurci azukatan masu yinta.
12. Mummunar cikawa idan ba'a tuba ba.
13. Duhun Qabari ga kuma azaba.
14. Kunyatarwa afilin Alkiyamah.
15. Mummunar makoma.
Ya Allah ka kiyayemu daga sharrin ZINA da dangoginta, da kuma dukkan abinda yake da nasabah da ita.