Akwai wani JINNUL ASHIQ wanda ya shiga jikin wasu 'Yan mata guda biyu, 'yan gida daya. Wai ya biya sadakinsu zai auresu gaba daya..
Idan ana yin addu'a akan guda daga cikinsu, zai rika Eehu ta bakinta, kuma yana dariya ta bakin 'Yar uwarta... Haka aka ci gaba da fama har Allah ya taimakemu akansa ya fita ya barsu.
Akwai Kuma wani saurayi wanda Wasu Matayen Aljanu guda biyu daga cikin Sarakunan Aljanu suka aureshi, Kowacce daga cikinsu ta haihu tare dashi (Kamar yadda suka fada).
Kuma suna kawo mishi yaran yana ganinsu agabansa duk lokacin da yake zaune adakinsa shi kadai..
* Akwai kuma lamarin wata baiwar Allah wacce wani kafirin Aljani ya aureta, Sun haifi yara hudu alokuta daban daban.
Zata ji alamar kamar tana dauke da juna biyu, amma idan ta duba ba zata ga komai ba..!!
Irin wadannan Labarurrukan suna da yawa sosai. wanda bai san abun ba, zai ga kamar ba haka bane. Amma duk wanda ya taba cin karo da masu irin wannan matsalar zai ga abinda yafi haka ma.
Allah ya kiyayemu, Allah ya bama marassa lafiyanmu lafiya.
WASSALAM.