Ba mutuwa nake tsoro ba, Sai dai ina duba Qarancin Guzurina ne. Da nauyin zunubina, Gashi kuma tafiyar tana da nisa!!
Kuma Ubangijinmu yayi rantsuwa mai ban tsoro!!
Yace: "INA RANTSUWA DA UBANGIJINKA (YA MUHAMMADU) WALLAHI SAI NA TASHESU! SANNAN KUMA WALLAHI SAI NA HALARTO DASU SUNA GURFANE AGEFEN JAHANNAMA"
Sannan na dubi yawan laifukana, gashi kuma Ubangiji yace "DUK WANDA YA AIKATA MISALIN NAUYIN KWAYAR ZARRAH NA SHARRI, SAI YA GANSHI"
Wannan Ayar tana razana dukkan mai hankali, kuma tana firgita tunanin Masu Tunani.
Idan kana gadarar cewa kai akan hanya Madaidaiciya kake, shin kana da tabbacin cewa Allah yana karbar Sallarka da sauran ayyukanka?? Ko kuwa nadeta akeyi ajefeka da ita akan fuskarka?
Kowanne bugawar second na agogo, Ajalinka yana Qara kusantowa... Amma kai kuma Zuciyarka tana Qara Kwadaita maka zaman duniya!!!!
Shaitan yana Qara mantar dakai Girman zunubbanka da kuma yawan laifukanka!!
"YA KAI DAN ADAM !! MENENE YA RUDAR DAKAI DAGA UBANGIJINKA MAI GIRMA?"
Ni dai Wallahi na kasa tunowa da wani aikin da nake da tabbas akansa ranar lahira....
Sai dai Imani da Allah, da kuma Son Manzon Allah (saww) da ahalin gidansa da Sahabbansa!!