Binciken da gidauniyar da ke nazari kan bacci ta kasa a Amurka ta gudanar ya nuna cewar kowanne mutum na bukatar bacci na wasu awowi bisa la'akari da shekarunsa.
Awa nawa kake bukata?
Ana son manyan su dunga baccin awa 7 zuwa 9.
Galibin mutane suna ganewa idan ba su samu isasshen bacci ba- to amma ana koshi da bacci?
Wani binciken da aka gudanar a Amurka ya nuna cewa shekarun mutum ne ke fayyace baccin awoyin da yake bukata.
Rashin atisaye, da shan giya da abubuwan da ke kara kuzari kamar su gahwa da abubuwan sha da agogo mai kararrawa na daga cikin abubuwan da ke rage baccin mutum a kullum.
Jarirai sun fi kowa bukatar bacci, suna bukatar baccin awa 19 a kullum.
Gidauniyar da ke nazari kan bacci a Amurka -- wacce ke Arlington da ke Virginia -- ta ce yanayin rayuwar mutum shi ne abin da ke sa wa a fahimci awoyin da yake bukata na bacci, amma kuma akwai shawara bisa shekarun mutum.
*.Jarirai (Zuwa wattani 3):A bisa tsari, sabon jariri na bukatar baccin awa 14 zuwa 17, amma dai baccin awa 11 zuwa 13 ya ishe shi.
Ba a ba da shawarar a bar jariri ya yi baccin fiye da awa 19.
*.Jarirai (Watanni 4-11):An ba da shawarar su yi baccin awa 12-15. Amma akalla baccin 10 ya ishe su.
Kuma ka da a bar su su yi baccin da ya wuce na awa 18.
*.Yaro (Dan shekara 1 zuwa 2):An ba da shawarar cewa yaron da ke rarrafe da wanda bai dade da soma tafiya ba na bukatar baccin awa 11 zuwa 14, amma baccin 9 zuwa 16 ya ishe shi.
*.Yaro (Dan shekara 3 zuwa 5):Kwararru sun ba da shawarar yaron ya yi bacci awa 10-13. Amma bai kamata ya yi bacci kasa da awa 8 ko fiye da awa 14.
*.Yaro (Dan shekaru 6 zuwa 13):Gidauniyar ta ba da shawarar baccin awa 9 zuwa 11 ga yaron da ke tsakanin wadannan shekarun. Amma bai kamata ya yi bacci kasa da awa 7 ko fiye da awa 12.
*.Matasa (Shekaru 14 zuwa 17 ):An ba da shawarar baccinsu ya kasance tsakanin awa 8 zuwa 10. Gidauniyar ta yi gargadin cewa baccin kasa da awa 7 ko fiye da awa 11 na da matsala ga lafiya.
*.Matasa (Shekaru 18 zuwa 25): An ba da shawarar baccinsu ya kasance tsakanin awa 7 zuwa 9.
Gidauniyar ta yi gargadin cewa baccin kasa da awa 6 ko fiye da awa 11 na da matsala ga lafiya.
*.'Yan shekaru 26 zuwa 64:Dai dai dana matasa.
*.Tsofaffi 'yan shekaru 65 zuwa sama:Su rika yin bacci na awa 7 zuwa 8 a kullum, amma ba a son ya gaza awa 5 ko kuma fiye da awa 9.
Bacci na da muhimmanci
Rashin bacci na janyo matsala ga lafiya
Kwararru kan bacci sun wallafa shawarwari game da bacci kamar haka:
1.Ka samu lokacin bacci iri daya ko da a karshen mako ne.
2.Ka dinga hutawa a kan gado
3.A yi atisaye a kullum
4.Tabbatar da cewa yanayin dakin (zafi/sanyi) ba zai cutar da kai ba
5.A yi bacci a kan katifa mai kyau da kuma matashin kai
6.Guji abubuwan da ke hana bacci kamarsu giya da kwaya
7.Kashe na'urorin lataroni kafin ka kwanta.
NI KUMA ADMIN ZAKI NACE SHAWARA NA KAWOMUKU SAI KU DUBA KU AUNA