YA RABBI muna Tawassuli da kaunar da muke yiwa Shugaban Annabawanka da Manzanninka, Masoyinka wanda kafi so, YA RABBI ka dubemu da Rahamarka, Ka yaye mana Wannan matsanancin halin da muke ciki a Nigeria.
YA RABBI kamar yadda ka amshi addu'ar Annabinka Nouhu ka tseratar dashi tare da mutanensa, sannan ka hallakar da dukkan Makiyansa, YA RABBI ka gaggauta hallakar da duk wanda yake yiwa addininka Makarkashiya awannan Qasar tamu.
YA RABBI Kamar yadda ka amshi addu'ar Annabinka AYYOOB ka bashi lafiya bayan jinyar da yayi, kuma da dawo masa da iyalansa da dukiyarsa, kuma ka ninninka masa, YA RABBI Muna rokonka ka warkar da al'ummar Musulmai daga chutar Munafurci da hassada da kwadayin Duniya.
Ka dawo mana da Arzikinmu da zama lafiyanmu, da hadin kanmu, kayi mana maganin duk abinda yake rarraba kawunanmu.
YA RABBI Kamar yadda ka amshi addu'ar Annabinka DHUN-NUUNI (YUSUS) Ka tseratar dashi daga cikin Kifin da ya hadiyaeshi, kuma ka yaye masa damuwarsa da bakin cikinsa, YA RABBI muma gamu cikin duhun Zunubai sun hadiyemu, YA RABBI ka tseratar damu ka gafarta mana, sannan ka yaye mana damuwarmu da bakin cikinmu ka kawo mana Sauyi na Alkhairi arayuwarmu da addininmu da zamantakewarmu.
YA RABBI Kamar yadda ka amshi addu'ar Annabinka YA'AQUUBU (AS) ka dawo masa da 'Dansa Yusufu kumq ka mayar masa da ganinsa bayan ya makance, YA RABBI amshi rokonmu da dawo mana da Shugabanni Nagari wadanda zasu rikemu da adalci, Kuma ka bude mana idanuwan zukatanmu mu rika ganin gaskiya, kuma muna aiki da ita.
YA RABBI kamar yadda ka amshi addu'ar ANNABINKA MUSA (AS) ka Qarfafeshi da Waziri nagari, sannan ka tseratar dashi daga FIR'AUNAN ZAMANINSA, YA RABBI ka Qarfafi Shugabannin da zaka bamu, ka basu Wazirai nagari, kuma ka tseratar damu daga FIR'AUNONIN ZAMANIN NAN NAMU wadanda kullum kullum duniyarsu ce agabansu, ba wai addininsu ko al'ummarsu ba.
Kayi musu yadd kayi ma wancan Fir'aunan Mutukar rayuwarsu ba zata zama alkhairi garemh ba.
YA RABBI kamar yadda ka amshi addu'ar Shugaban bayinka, ya Fiyayyen Annabawanka, Shugabanmu Muhammadu (saww) ka tseratar dashi daga kowanne tuggu da makircin Makiyansa na cikin gida da waje, Sannan ka Azashi bisan dukkan Makiyansa aranar Badar da Uhudu da Muraisee'u da Khaybar da Hunainu, da ranar Fat'hu!!
YA RABBI muna tawassuli da wannan nasarar da ka bashi, Muma ka Aza-mu bisa dukkan Makiyanmu na cikin gida da waje, kar ka basu nasara akanmu, kar ka faranta musu rai akanmu.
Ka amshi rokonmu don albarkar Sunanka "AL-AZEEZU" MABUWAYI, MAI NASARA WANDA BA'A RINJAYARSA..
Sallal-Lahu 'alan Nabiyyi wa aali baitihi wa sahbihi wat-tabi'een.