Lallai nasan mutane da dama burin su ya cika na ganin cewar Muhammadu Buhari ya zama zababben shugaban kasar Najeriya.
Wannan wani budi ne daga Allah madaukakin sarki, kuma wannan nasara ba ta mutanen Arewacin Najeriyar ba ne, sai dai na mutanen Najeriya ne baki daya.
Amma kuma duk mutumin da Allah Ya bashi mulki a hannnunsa, ba bu abin da yake son illa a taya shi da Addu'o'i ta kowace fuska. Duk lokacin da na ga cewar saura 'yan kwanaki ayi zaben shugaban kasa, abin da nake kokarin rokon Allah shine Allah kada ya jarabe mu da abubuwan da malamai su ka hango zai iya faruwa sakamakon tsayuwar GMB da GEJ.
Amma da yake Allah - Allah ne, baya shawara da kowa kuma tun kafin yayi dunya ya hukunta cewar za ayi zabe 2015 a 28 ga watan Maris kuma za ayi lafiya a gama lafiya.
Mutane da dama sun tsayu cikin dare suna rokon Allah Ya saukaka mana a cikin wannan zabe kuma Allah Ya saukaka. Sai dai 'yar nune ta nuna, tun kafin hukumar INEC ta fadi cewar Janar Muhammadu Buhari ya ci zabe, tuni wadansu suka bakunci lahira, ta hanyar yin wawta da abubuwan hawa. Wannan yake nuna cewar da Allah Ya kaddara ba GMB ba ne ya ci wannan zabe, ko shakka bana yi, wadannan yara sune wadanda za su kawo hargitsi da tarnaki a cikin garuruwansu.
Irin wannan maganar ce, dayawa daga cikin mutane ba sa so, kuma itace gaskiya, kuma ita gaskiya bata bukatar ado ko kuma salo. Akwai abubuwa da yawa da suka faru bayan wannan zabe wanda ya tabbatar mana da cewar da ba Janar ba ne, to, da mutane da yawa da an aikasu Lahira.
ME BUHARI YAKE BUKATA
Kun san ita siyasa mugun wasace, kowa da ka sani yana da manufa a cikin rayuwarsa. Wasu wannan nasara da aka samu, sun tabbatar karshen zaluncinsu ya zo karshe, wasu kuma kakarsu ce suke ganin ta yanke saka.
Akwai masu boyayyiyar manufa kuma suna tare da shi wannan mutumin, kuma ban da Allah babu wanda ya san wace irin manuface, kamar yadda lokacin da shugabancin kasar ya dawo Arewa ashe akwai boyayyiyar manufa ba mu sani ba sai kawai muga tsinci kanmu a kashe-kashe da tashe-tashen bama-bamai.
Wasu sabbabin Addu'o'i za mu koma kuma muna yiwa wannan bawan Allah, kamar yadda shi da ya fi sanin irin hakki da Allah Ya daura mishi yayi wuf ya wuce kasa mai tsarki, domin neman gafarar Allah saboda abin da ya yi a lokacin neman zabe, tun da daman yaki dan zamba ne. To mun fayi zamba har da rawar banjo kafin su amince cewar nawan ba mai ra'ayin rikau bane.
Addu'ar tsawon rai, da koshin lafiya, da kuma Allah Ya tabbatar da shi akan abin da shi Allah Ya ke so kuma Ya yarda da Shi kai ya ke bukatar mu ta roko.
Dukkanin wani makirci da ake kullawa a cikin dare da rana, a sarari da boye, a kusa da nesa, Allah Ya tsare shi. Na ragowar kanakin da ya rage a rantsar da shi da bayan rantsar da shi, Allah Ta'ala ya wargaza su.
Yana bukatar yi mishi addu'ar abota da mutanen kwarai, Mu yi mishi addu'ar Allah Ya kusanto da wanda ya ke nesa da shi amma kuma alheri ne a tafiyarsa. Ya kuma nisantar da duk wanda yake mugu ne kuma munafiki ne dake jikinsa, nisannisan Sammai da kassai.
Yana bukatar mu taya shi rokon Allah ya bashi ikon sauke nauyin da ke kansa, ya shinfida Adalci ga kowa da kowa. Musulmi da Kirista da ma wadanda suka ce basu da Addini. Ya bashi hakuri da irin cutarwar da mu za mu yi mishi.
Idan kai mai son Janar Buhari ne, to ka yi kokarin yin wadannan abubuwa domin samun sauki, da nasara a gare shi.
Allah ka amsa bukatun mu, ka kuma warware mana matsalolinmu, ka yafe kurakuranmu, ka karfafe mu, ka nauyaya mizaninmu, ka haskaka al'amuranmu, ka yalwata mana arzikinmu, ka gafartawa iyayenmu da 'yan uwanmu da malamanmu, da sauran al'umma baki daya, ka kara salati da aminci ga Annabinka Muhammud Sallalahu Alaihi Wa Sallam, da Iyalansa da Matayensa, da Sahabbansa da wadanda suka bishi da gaskiya har zuwa ranar kiyama amin.
Salisu Hassan (Webmaster)
Babban Edita
Mujallar Duniyar Computer
Title :
ABUBUWAN DA BUHARI YA KE BUKATARSU A YANZU
Description : Lallai nasan mutane da dama burin su ya cika na ganin cewar Muhammadu Buhari ya zama zababben shugaban kasar Najeriya. Wannan wani budi ne ...
Rating :
5