Kar ka damu da hassadar masu hassada, Kar ka rama muguntar Masu mugunta... Kar ka hana masu Gulma suyi aikinsu akanka...
Da Mahassadanka da Makiyanka na fili da na boye, da Magulmatanka, duk wadannan Allah ya horesu gareka ne domin taimakonka wajen gyaran tafiyarka..
Shi mai hassada, Hassadarsa kansa take komawa. Kai kuma ayyukansa na alkhairi gareka zasu dawo. Da sannu sai Allah ya dusashe haskensa, kai kuma naka hasken ya daukaka.
Da ace mai hassada ya san alkhairin da hassadarsa take jawo maka, Wallahi da sai ya juyar da hassadar ta koma kansa ko kuma kan 'ya'yansa.
Shi kuma Makiyyi, Ubangiji yace ka rikeshi tamkar Babban masoyinka. ka kyautata masa, ka girmamshi, da sannu kiyayyarsa zata juye ta zama soyayya mai karfin gaske...
Shi kuwa mai GULMA, 'dayan cikin biyu ne. Idan abinda yake fada akanka gaskiya ne, to kaga kenan ya bankado laifinka afili sai ka gyara.
Idan kuma Qarya yayi maka, to kaga ka samu ladan zaluntarka da yayi kenan... Kuma ka samu damar kiyaye abinda yake fada kenan.
Kuma samun irin wadannan mutanen arayuwarka yana nuna cewa rayuwar taka zatayi ne. domin kuwa wadanda rayuwar tasu babu wani haske, ba zasu samu mai yi musu hassada ba.
ALLAH ya sanya maka su ne domin kar ka dogara da halittunsa wajen neman ci gaban rayuwarka. ka mika dukkan lamarinka zuwa ga Allah. Shine fiyayyen abin dogaro.
DAGA ZAUREN FIQHU.