Yan uwana mudaina raina Qananan zunubai, kada mudinga duba Qanqantar laifin, A‘a muri‘ka duba girman wanda muke sa‘bawa Shine ALLAH (subhanahu wata‘ala).
Kuma Qananan zunuban (saga‘ir) da muke rainawa, idan ba tuba mukeyi ba, sune wata rana zasu taru su zama gingima gingiman zunubai (kaba‘ir).
Domin Manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam) yabuga mana misalin Qananan zunubai da masu rura wuta.
Inda yake cewa:-
Inayi muku Kashedi da tara Qananan zunubai, domin kwatan kwacinsu (‘kananan zunubai) kamar kwatan kwacin wasu ayarin matafiyane, da suka sauka a (wani gari), wannan yazo da ice, wannan yazo da ice, wancan yazo da ice, sannan idan suka tarasu da yawa, saisu hada wuta gagaruma!
AHMAD A HADITH(3808-22302).
Yaku ‘Yan uwana wannan shine kwatan kwacin Qananan zunubai daga bakin farin jakada, shugaban halittu gaba ‘daya annabi muhammad (sallallahu alaihi wasallam).
Allah muke roqo yayafe mana laifukanmu, wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba.