TAMBAYA TA 1550
*******************
Assalamu alaikum,
Malam Allah swt ya saka da alkhairi. Malam meye hukuncin tsagaitawa bayan kammala karatun fatiha kafin surah acikin sallah, ma‘ana dan shiru da liman yake yi bayan karatun fatihah kafin ya soma karatun surah. Bissalaam
Daga (Auwal A A).
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh.
Eh gaskiya ne akwai ingantancen hadisin da ya nuna cewa Manzon Allah (saww) ya kan yi shuru bayan kabbarar harama kafin ya fara karatun fatiha. Sannan kuma yakan yi shuru bayan ya kammala dukkan karatu kafin yayi ruku'u.
Amma hadisin da yazo da maganar yin shuru tsakanin karatun fatiha da surah, wannan bai kai inganta ba. Hatta malaman Fiqhu ma suna yin taqaddama akansa.
Don haka Mazhabin Shafi'iyyah ne kawai suka ce Sunnah ne yin hakan bisa liman saboda Mamunsa su samu damar yin karatun fatiha. Kamar yadda Imamul Baajuriy ya kawo acikin HASHIYA juzu'i na 1 shafi na 166. da kuma QAULUT TAAMMI na Ibnul Imaad, juzu'i na 1 shafi na 17.
Don haka tunda hadisin bai inganta ba, bai zama wajibi gareka kayi aiki dashi ba. Malaman da suke aiki dashi dinma sun daukeshi amatsayin Mustahabbi ne.
WALLAHU A'ALAM.