Sunan mahaifin Annabi (s.a.w) Abdullah dan Abdul Mudallabi, sunan Abdul mudallabi (shaibah) dan Hashim, sunan hashim Amru, dan Abdul Manaf, har zuwa kakansa na 20 Adnan.
Tsakanin Adnan zuwa Annabi Isma'ila dan Annabi Ibrahim, har zuwa Annabi Nuhu, zuwa Annabi Adam, wasu malaman tarihi sun kawo sunayen su duka har zuwa Annabi Adam, amma abin dayafi inganci da tabbata shine zuwa kan Adnan.
Amma an tabbatar cewa duk wadanda suke cikin nasabar Annabi (s.a.w) nagartattun mutane ne masu mutunci da kamewa da asali.
Mahaifiyarsa sunanta Amina yar wahbi, daga banu zuhrata, sun hadu da mahaifinsa a nasaba ta wajen kakansa kilab dan murrata, shi Annabi (s.a.w) shi kadai ne a wajen mahaifinsa da mahaifiyarsa.
Ya Allah kaqara tsira ga shugabanmu Annabi Muhammad (s.a.w).