Wannan shine abinda ZAUREN zai tattauna akansa yanzun nan Insha Allah.
Hakika muminai zasu ga Ubangijinsu QURU-QURU afilin Alkiyama, kuma zasu ci gaba da ganinsa acikin Aljannah. (Allah yasa muna da babban rabo).
Acikin Alqur'ani Allah yana cewa:
"WASU FUSKOKIN MASU HASKE NE AWANNAN RANAR. MASU KALLO NE ZUWA GA UBANGIJINSU".
(suratul Qiyamah ayah ta 22-23)
Malaman tafseeri suka ce "ZASU GANSHI NE QIRI-QIRI".
Kamar yadda Imamul Bukhary ya ruwaito acikin Sahih nasa, akan lambar hadisi na 7,435.
Manzon Allah (saww) yana cewa: "HAKIKA KU DA SANNU ZAKU GA UBANGIJINKU QURU-QURU".
Kallon da Muminai zasu yiwa Ubangijinsu, ya tabbata acikin Sahihan hadisai masu yawa sosai daga Manyan Maluman hadisi.
1. Hadisi Sahihi daga Sayyiduna Abu Huraira da Abu Sa'eed Alkhudry (Allah shi yarda dasu) sun ce:
"Wadansu mutane sun tambayi Manzon Allah (saww) – "Ya Rasulallahi shin zamu ga Ubangijinmu ne aranar ALQIYAMAH?".
Sai yace "SHIN KUNA KOKONTON GANIN HASKEN RANA DANA FARIN-WATA WANDA WANI GAJIMARAI BAI TARE SU BA?"
Sai suka ce "A'a". Sai yace "TO HAKANAN ZAKU KALLI UBANGIJINKU".
Aduba cikin Sahihul Bukhariy hadisi na 7,437. Sahihu Muslim hadisi na 182.
2. Sayyiduna Jareer (ra) yace : "Manzon Allah (saww) ya kalli farin wata adaren sha-hudu (wato daren da watan yake Qure haskensa) sai yace:
"ZAKU KALLI UBANGIJINKU KAMAR YADDA KULE KALLON WANNAN FARIN WATAN.
IDAN ZAKU IYA KOKARIN KUGA BA'A RINJAYAR DAKU DAGA YIN SALLAH KAFIN HUDOWAR RANA, DA KUMA KAFIN FADUWARTA BA, TO KU AIKATA HAKAN"
Sahihu Muslim hadisi na 633. Sahihul Bukhariy hadisi na 7,434.
3. Daga Abu Musal Ash'ary (ra) yace Manzon Allah (saww) yace:
"AKWAI ALJANNATAI GUDA BIYU NA ZINARE, KWANUKAN CIKINTA DA DUKKAN KAYAYYAKIN CIKINTA (NA ZINARE NE).
DA KUMA WASU ALJANNATAI GUDA BIYU NA AZURFA NE KWANUKAN CIKINSU DA DUKKAN KAYAN CIKINSU (NA AZURFAN NE).
BABU ABINDA KE TSAKANIN MUTANE DA KUMA KALLON UBANGIJINSU IN BANDA MAYAFIN NAN NA GIRMANSA BISA ZATINSA. ACIKIN JANNATU ADNIN"
- Sahihul Bukhariy hadisi na 4,878. Sahihu Muslim hadisi na 180.
4. Hadisi daga Sayyiduna Suhaibur Rumiy (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"IDAN 'YAN ALJANNAH SUN SHIGA ALJANNAH SAI UBANGIJI YACE MUSU :
"SHIN AKWAI WANI ABINDA KUKE SO IN QARA MUKU?
Sai suce "(YA RABBI) Shin baka Faranta fuskokinmu ba! Shi baka shigar damu aljannarka kuma ka tseratar damu daga shiga wuta ba!!
Daga nan sai Allah ya yaye musu Hijabi (sai su ganshi). Kuma babu wani abu mafi soyuwa agaresu cikin dukkan abinda aka basu fiye da wannan kallon nasa. wannan shine Qarin da Allah yake nufi wanda ya fada acikin Alqur'ani.
- Sahihu Muslim hadisi na 181.
5. Daga Sayyiduna Abdullahi bn Umar (ra) yace Manzon Allah (saww) yace :
"MAFI QANKANTAR MATSAYI DAGA CIKIN 'YAN ALJANNAH ZAI YI SHEKARU DUBU BIYU YANA KALLON WAJEN DA YA MALLAKA (WATO GIDAJENSA NA ALJANNAH) YANA KALLON WURI MAFI NISA KAMAR YADDA GANIN NA KUSA DASHI. KUMA YANA KALLON MATAYENSA DA HADIMANSA.
KUMA MAFIFICIN MATSAYI ACIKINSU ('YAN ALJANNAR) ZAI RIKA KALLO ZUWA GA ZATIN ALLAH NE HAR SAU BIYU AKULLUM"
- musnad juzu'i na 2 shafi na 13. Tirmizy hadisi na 3,330.
Ganin Ubangiji abu ne tabbatacce acikin Alqur'ani da Sunnar Manzon Allah (saww). Kuma dukkan Maluman Musulunci sunyi ittifaki akan haka.
Ya Allah kasa muna daga cikin masu ganinka afilin Alqiyamah, da kuma gidan Aljannah. Musa kusa da babban Masoyinmu (saww).
An gabatar da karatun ne acikin ZAUREN FIQHU WHATSAPP 2 da 4.