Assalamu alaikum. girma da daukaka su tabbata ga shugabanmu annabi Muhammadu s.a.w da ahlin gidansa da sahabbansa tsarkaka.
Malam alkairin Allah ya tabbata agareka da sauran daukakin al'umar musulmi baki daya.
Tambaya itace Nasan mutum me janaba ze iya zikiri, tasbihi da salati..Malam shlhin mace me haila itama zata iya aikata hakan?
2, mutun ne ke zargin matarsa da yawan fita (unguwa) har ta kai ga ya saketa, in yana da bukatar mayar da ita ze iya?
3, ina bukatar malam da yaja hankalin en mata akan Half naked dress.
wlh malam mu dake akasuwa muke ganin irin hatsabibiyar shigar dasuke abun kyama da kunya ne ga 'ya'yan musulmi.
AMSA
******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Ai hukuncin haila da janaba yakan zama iri guda acikin mafiya yawan mas'aloli.
Bisa mazhabin Limamin gidan Hijira (Wato Imamu Malik) Ya halatta mace mai haila tayi kowanne irin zikiri. harda tilawar Alqur'ani (amma ba tare da ta ta'ba Mus'hafin Alqur'anin ba).
2. Mutumin da yake zargin cewa matarsa tana fita waje, har wannan zargin ya kai ga rabuwar aurensu, yana da damar ya sake dawo da ita amatsayin matarsa in dai sakin da yayi mata bai kai uku ba.
Amma wasu Malaman sunce in dai zargin Zina yake yi mata, to babu damar ya sake mayar da ita matarsa har sai ya tuba daga wannan zargin da yake yi mata.
Saboda shi Musulunci ba ya son zaman chutuwa. mutukar yana ci gaba da zarginta da zina, zai yiwu watarana idan ta haihu yace wannan yaron ba nasa bane. kaga kenan sai sunje sunyi Li'aani.
3. Matayen da suke yin mummunan dressing, hakika Allah da Manzonsa ya tsine musu. Kuma Manzon Allah (saww) yace bw zasu shiga aljannah ba. kuma koda Qamshinta ma ba zasu ji ba.
Kuma wannan alama ce da take nuna cewa sun riga sun amincr da fushin Allah, sun yarda cewa su ribatattun Shaitan ne. Shi yasa ba zaka ga wani mutumin kirki yana kulasu ba. Sai dai Qazamai masu Qazantar tunani irin nasu.
WALLAHU A'ALAM