Nuna ladabi ga Shugaban Halitta (saww) Wajibi ne. Kuma yana daga cikin manyan katangun da suke tsare Imanin mutum daga zubewa.
Allah (saww) ya hana mu rika kiran sunan Manzon Allah (saww) kamar irin yadda muke kiran junanmu. Allah yana cewa:
"KAR KU SANYA KIRAN MANZON NAN ATSAKANINKU KAMAR YADDA SASHENKU SUKE KIRAN SASHE".
Wato Haramun ne ka kira sunansa 'GAYA' kamar yadda kake kiran sunan Qaninka ko abokinka.. Kuma HARAMUN NE ka cira muryarka wajen kiransa..
Sannan Allah ya hana Sahabbai su rika fara yin magana Kafin Manzon Allah (saww) kuma ya hana su rika magana da karfi agabansa.
Sakamakon duk wanda ba ya nuna ladabi ga Manzon Allah (saww) shine KAFIRCI da ZUBEWAR IMANINSA ba tare da Saninsa ba.
Ya Allah ka kiyayemu daga asarar Imaninmu.