Babban kuskure ne gareki amatsayinki na 'Ya mace ki rika nuna ma saurayi kwadayin kudinsa afili. Kina kawo masa bukatunki, ya saya miki wannan, ya saya miki wancan, ya baki kudin dinki, kudin anko, kudin party, etc..
Da zarar saurayi ya biya miki bukatarki ta kudi, to shi kuma zai fara kwadayin kema DOLE ki biya masa bukatar sha'awarsa..
* HARAMUN NE, BAI HALATTA BA, ku rika zama daga ke sai saurayinki.. Komai Ustazancinsa, komai yawan soyayyar dake tsakaninku, Shaitan ne zai zama na ukunku.. Zai shiga zuciyarsa ya rika Qawata masa cewa yayi zina dake.. kema haka..
* TSINUWAR ALLAH DATA MALA'IKUNSA ta tabbata bisa duk budurwar da zata sanya kaya matsatsu masu nuna siffar Nononta ko bayanta, Sannan ta fesa turare ta tafi wajen saurayi...
Annabi (saww) ya tsine ma mataye masu irin wannan shigar.. Kuma yace ba zasuji koda Qamshin aljannah ba!!!
* AZABA MAI RADADI DA WULAKANTARWA ta tabbata bisa budurwar da take SEX-CHAT (chatting na batsa) da wani saurayi.. koda kuwa ya kai mata sadaki.. Allah zai kwashe albarka gareshi shi da ita...
* Kunyar duniya da kuma FALLASA ARANAR TSAIWA ta tabbata bisa dukkan budurwar da ta bama saurayi jikinta yana ta'bawa, ko kuma ta bashi dama yayi zina da ita..
Daga wannan ranar taci amanar Allah da Manzonsa da amanar iyayenta da danginta.. Kuma ta fidda kanta daga layin mutane masu albarka masu Qima awajen Allah.
Addu'ar ZAUREN FIQHU ita ce: Allah yasa wannan rubutun ya zama sanadiyyar shiryuwar bayin Allah wadanda suka afka cikin wannan babbar hallaka.. Wadanda basuyi kuma, Allah ya kiyayemu baki daya.