Mutanen da Allah yafi so acikin bayinsa, sune wadanda suke da zuciya mai tsafta..
Zuciyar da take wanke tas!! babu hassada ko kyashi ko girman kai ko mummunan zato acikinta..
Hakika aranar lahira mutane da yawa zasu sha mamaki. domin kuwa zasu iske cewa Allah ba ya karbar mafiya yawan ayyukansu saboda rashin kyawun zukatansu.
Babu aiki mafi tsada mafi daraja awajen Allah kamar kyawun dabi'a... ita kuma bata samuwa sai wajen mutanen da zuciyarsu ta tsarkaka...
Allah babu ruwansa da siffarka.. ayyukanka yake kallo da kuma zuciyarka.. idan aikinka yayi kyau, kuma zuciyarka tayi kyau shikenan Allah zai karba... amma idan zuciyarka ta zam mummuna, komai kyawun aikinka Allah ba zai karba ba..
Allah mai tsarki ne. ba ya karbar ayyuka sai masu tsarki wadanda tsarkakakkun bayinsa suka aikata.
'Yan uwa mu bada muhimmanci sosai wajen gyaran zukatanmu. Shine zai zama mafita agaremu.
ZAUREN FIQHU.