Assalamu Alaikum Allah ya taimaki malam tambayata shine mijina ya rasu ne a prison banji labariba sai bayan shekara daya da Rabi to shin malam zanyi takaba ne a lokacinnan da naji ko kuwa aa lokacin ya wuce.
Saboda Na tambayi malamai biyu Na farkon yace babu likacin ya wuce Na biyu kuma yace a a zan fara takaba ne a lokacin da kunne na yaji rasuwarsa to malam I'm confused Na rasa wanne zan bi ka taimakamin da bayani Allah ya sakawa malam Amin.
(daga wata baiwar Allah).
AMSA
******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Maganar da malamin farko ya gaya miki haka take. Zaki fara lissafin kwanakin takaba ne daga lokacin rasuwarsa. Misali idan ya rasu ne tun watanni hudu da suka wuce, to kinga takabar kwana goma kachal zakiyi. tunda dama kwanakin takaba wata hudu ne da kwana goma.
Idan kuma baki samu labari ba, har lokacin takabar ya riga ya wuce, (kamar yadda kika ce sai bayan shekara guda kika samu labari) to shikenan takabarki ta riga ta Qare. Ko yanzu kika samu wani mijin zaki iya daura aure dashi.
Da fatan Allah ya jikan mijinki, ya gafarta masa. yasa mutuwar ta zam hutu agareshi. mu kuma idan tamu tazo, Allah yasa mu cika da kyau da imani.
WALLAHU A'ALAM.