Manzon Allah (saww) ya bamu labarin cewa alokacin da yaje Mi'iraji ya leka cikin wuta, yaga wasu Mutane Tsirara, an tattarasu acikin wani tanderu (Ramin Dagwalon Azaba) wuta tana ci ta Qasansu, kuma Mala'iku suna Jibgarsu suna ci gaba da gaba musu azaba.
Sai ya tambayi Mala'ika Jibreelu "YA JIBREELU WA'DANNAN SU WAYE??"
Sai yace "WADANNAN MAZINATA NE".
Manzon Allah (saww) ya bada labarin cewa akwai wani irin eehu da kururuwa wanda 'Yan wuta suke yi an bude musu Farjojin Mazinata.
Kunji fa, saboda tsananin wari da 'doyin al'aurar Mazinata, idan an budeshi sai dukkan 'Yan wuta sunyi ta eehu suna kururuwa.
Hakanan akwai wani ruwa mai bala'in wari wanda yake fitowa daga cikin al'aurar Mazinata idan ana yi gana musu Azaba.
Wannan ruwan sunansa "TEENUL KHABAAL". Yana daga cikin nau'in abincin da 'Yan wuta suke ci.
Ya ku Jama'a mu Guji Zina da dukkan dangoginta, wallahi Zina Bala'i ce aduniya da lahira.. Ya Allah ka tsaremu.
___ FROM ZAUREN FIQHU ____