Allah shigafarta malam naji wata magana ne yau kuma ina shakku akai wai Namiji zai iya yin kitso a kansa ba haramun bane?
(Daga wani bawan Allah).
AMSA
******
Dangane da yin kitso ga mazaje ko kuma barin gashinsu haka, abu ne wanda addini bai tsananta akai ba.
Domin kuwa an ruwaito cewa Annabi (saww) yakan bar gashin kansa ne asake ba tare da kitso ba.
Sannan kuma an ruwaito cewa ya ta'ba raba Sumar kansa kashi hudu, sai ya kitsesu daban daban.
Sayyiduna Abu Huraira (ra) ya ruwaito Manzon Allah (saww) yana cewa: "Duk wanda yake da Gashi, to ya kula (ya tsaftace) abinsa".
(Abu Dawud hadisi na 4163).
Manzon Allah (saww) shi kansa yana da gashi mai tsawo har zuwa kan kafadunsa. (Kamar yadda Imam Bukhary ya ruwaito daga Anas bn Malik, ahadisi mai lamba 5563 da kuma Sahihu Muslim hadisi mai lamba 2338.
Har ma wani lokacin matarsa Sayyidai A'isha takan taje masa gashin kamar yadda Imamul Bukhary ya ruwaito a hadisi na 219.
Imam Tirmizy da Abu Dawud da Ibnu Maajah sun ruwaito hadisi daga Sayyidah Ummuhani (ra) tana cewa Manzon Allah (saww) ya shigo garin Makkah alhali akwai kitso guda hudu akansa".
Da yake shin Sharhi akan wannan hadisin, Ibnu Hajr Al-askalani yace : Wannan hadisin na Sayyidah Ummuhani za'a daukeshi ne amatsayin cewa ba wai ko yaushe yake yin kitson ba.
Yakan yi ne alokacin da bai samu damar Tajewa ko kula da gashin sosai ba, saboda halin tafiya, ko yaki.
Ba wai abu ne na yau da kullum ba.
(FATHUL BAAREE, mujalladi na 10 shafi na 360).
Awancan lokacin nasu, ba abun mamaki bane don mutum namiji yayi kitso. Amma alokutan da suka biyo bayan wannan, sai abun ya zama ba al'adar Mazaje ba.
Don haka idan mutum ya tsinci kansa agarin da maza masu mutunci suna yin kitso shikenan babu laifi yayi.
Amma idan ka tsinki kanka agarin da Mazaje masu Mutunci basu yin kitso, to bai kamata kayi ba.
Mu dai anan yankin Nigeria bamu saba ganin Maza manya masu mutunci suna yin kitso ba. Sai dai Mawakan turai, ko 'yan Kwallo da dai sauransu.
Bai kamata mutum yayi koyi dasu ba. Domin kuwa duk wanda yayi kama da wasu mutane to za'a tasheshi tare dasu aranar Alkiyama.
Wallahu a'alam.