Slm Allah gafarta malam inada tambaya in ina saduwa da matata saita dinga jin zafi kuma daga na kusanceta sai na biya bukatata cikin minti biyu ko uku malam atemaka mini da magani.
AMSA
******
Idan irin wadannan matsalolin suna faruwa ga ma'aurata ta kowanne bangare, to mafi kyawun mataki shine da kai da matar taka ku ziyarci wata cibiyar lafiya ta Islama mafi kusa daku domin ayi muku tambayoyi a fahimci ta inda matsalar take.
Zata yiwu wani daga cikinku yana fama da infection. Ko kuma Aljanun soyayya suna tare da wani daga cikinku.
Bayan Wadannan da na fada, akwai ma wasu dalilai da dama wadanda suke haifar da haka. sai anje Asibitin Musulinci ko na zamani za'ayi muku tambayoyi.
WALLAHU A'ALAM