TAMBAYA TA 1549
*******************
Assalamu alaikum malam! Ya jama'a? Allah ya saka maka da jannatul firdausi, amin. malam na gode da jawabin da kamun akan matsalar kuraje, Alhamdulillah na hada kuma na fara ganin sauki cikin ikon Allah.Yanzu malam matsalata daya ce duk randa muka raya sunnah da megida to da safe sai nayi ciwon ciki da ganin jini brown koda ace na gama al'ada da kwanaki ko sati. abun yana damuna kuma shin sai nayi wanka kafin inyi sallah? daga wata baiwar Allah.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuh.
Shi irin wannan jinin ba'a kirgashi amatsayin haila. tunda yana zuwa ne abayan kin riga kinyi tsarkinki na jinin haila.
Akwai hadisi Sahihi wanda Imamul Bukhariy da Abu Dawud suka ruwaito daga Sayyidah Nusaibah (Ummu Atiyyah) tace:
"MUN KASANCE (AZAMANIN MANZON ALLAH SAWW) BAMU KIRGA GAURAYAYYEN JINI DA KUMA FATSI-FATSI AMATDAYIN WANI ABU, BAYAN MUN RIGA MUNYI WANKAN TSARKI".
ABINDA TAKE NUFI: In dai irin wannan brown din ko yellow ya fito ne bayan mace ta riga tayi wankan tsarkin jinin hailarta, to ba zata kirgashi amatsayin haila ba. Amma idan acikin kwanakin hailarta ne, to zata yi la'akari dashi.
Saboda haka wankeshi kawai zakiyi idan kinje wankan janabah. idan kuma da rana ne sai kije ki sanya ruwa ki wankeshi kawai.
Amma bisa dukkan alamu watakil kina da matsalar ASHIQ ko kuma wani infection mai tsanani. domin wancan karon kinyi maganar Quraje, yanzu kuma ga wannan brown din wanda ba ya fitowa sai Maigida ya kusanceki.
Ya kamata kiyi masa bayani ku tashi tsaye ku nemi magani. Allah ya sawwake.
WALLAHU A'ALAM.