TAMBAYA TA 1544
*******************
Assalamu alaikum. Allah gafarta Malam menene hukuncin irin Mazan nan masu cin amanar matayensu?
Allah gafarta, irin amanar itace, sai mutum yabar matarsa agida ya fita waje yaci abinda yaga dama amma bai bar ma matarsa ko shinkafa cokali daya ba, sannan sai ya bar matarsa agida yaje yana neman matan banza.. miye hukuncin mai aikata wannan?
AMSA
******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh.
Farko dai ita mace amana ce ahannun mijinta. ya daukota daga gidan Iyayenta tare da shaidu kuma ya dauki alkawarin ciyar da ita da shayarwa da tufatarwa da ita gwargwadon wadatarsa. Don haka mutukar ya ajiye wannan nauyin yaki kulawa da ita alhali yana da abin da zai bata amma ya hana, to tabbas yaci amanar Allah da Manzonsa, kuma aranar lahira sai Allah ya tambayeshi akan wannan amanar.
Wani Sahabi ya tambayi Manzon Allah (saww) "Menene hakkin matar 'dayanmu akansa?" sau yace :
"KA CIYAR DA ITA IDAN KACI, KUMA KA TUFATAR DA ITA IDAN KA TUFATA KANKA....."
Hakika duk namijin da yake aikata wannan ya shiga sahun MAROWATA kenan. Ita kuwa rowa tana jan Sahibinta ne zuwa ga shiga wuta. Allah shi kiyayemu.
Abu na biyu: ZINA DA NEMAN MATAN BANZA: Wannan kam duk mai mutunci mai tsoron Allah ba zai aikata ba. Domin ita zina mummunar kaba'ira ce kuma tana gadar da talauci da kuma munafurci azuciyar masu yinta.
Acikin wani hadisi, Manzon Allah (saww) ya bada misalin irin wadannan Mazajen kamar Mutumin da yaje da Nama mai tsafta ne agabansa, amma yake tsallakeshu yana zuwa yana cin rubabben naman Mushe mai wari mai 'doyi.
Ya Allah ka shiryi maza da mata masu irin wadannan halayen. Mu kuma ka kiyayemu don hasken Alqur'aninka.
WALLAHU A'ALAM.