TAMBAYA TA 1546
*******************
bayan gaisuwa irin ta addinin musulunci, malam inama fatan alkaire bisa dunbun taimako da kakeyi, a wannan addin namu Allah yasa maka da alkairi.
malam wani abokina ne yake cikin wani hali wanda yake neman taimako, malam shi wannan bawan Allah yana fama da wani Irin wani abu, haka kawe malam MANIYYI yake fitomar haka kawe kuma baya yin ISTIMA'I, kuma yana kokarin yin azumi, to amma har yanzu abun yana damunsa shine muke neman temako daga ilimin da Allah ya horema. Allah yasaka, mal. don Allah aboye suna na.
AMSA
*******
Duk wanda yake fama da irin wannan matsalar ya samo Garin Habbatus Sauda cokali 7, Garin Kustul Hindi cokali 5, Garin Lalle cokali 1.
Ya hadasu waje guda acikin ruwan zuma yana shan cokali uku kafin ya kwanta barci. Sannan cokali 3 bayan ya karya da safe.
Insha Allah zai samu waraka da izinin Allah.
WALLAHU A'ALAM.