Dubban magoya bayan kulob din AC Milan ne suka kaurace wa karawar da ya yi da Cagliari a gida a gasar Seria A ranar Asabar.Magoya bayan kulob din sun kaurace wa wasan ne domin bayyana fushinsu kan yadda shugaba Silvio Berlusconi ke gudanar da kulob din.Sai dai kuma Milan ya samu nasara a karawar da ci 3-1, kuma nasarar ta sa ya koma mataki na bakwai a kan teburin Serie A.Ba a fitar da adadin 'yan kallon da suka shiga filin wasa na San Siro mai diban mutane 80,000 a ranar Asabar ba, amma yawancin kujeru babu 'yan kallo.
AC Milan ya lashe kofunan Serie A 18, kuma ya kammala gasar bana a mataki na takwas dalilin da yasa ya kasa shiga gasar kofin zakarun Turai ta bana.
Title :
Magoya bayan AC Milan sun kaurace wa wasa
Description : Dubban magoya bayan kulob din AC Milan ne suka kaurace wa karawar da ya yi da Cagliari a gida a gasar Seria A ranar Asabar.Magoya bayan kulo...
Rating :
5