TAMBAYA TA 1551
******************
Assalamu alaikum wa rahmatullahi ta'ala
wa barakatuhu. malam muna maka addu'ar Allah
ya jikan mahaifa Allah yasa agama lafiya.
Malam ni fatawata awannan shafi naka mai tarun albarka
shine, matsalata akan rashin gamsar da iyalina
wanda har ya kai takan yi tsuka da nuna fushinta afili
kuma hakan na tayar min da hankali matuka.
Dan Allah malam ataimaka nagode daga sabon dalibinka
Liman Umar Cheledi ba kunya amaganan neman
magani musamman bangaren gyaran gida domin
shine kundin tsarin mulkin gidan.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam Wa rahmatullahi Ta'ala wa barakatuh.
Su abubuwan da suke yin sanadiyyar mutuwar al'aurar 'Da Namiji suna da yawa sosai. Ga wasu daga ciki:
1. HAWAN JINI : idan kana fama da hawan jini zaka iya samun raunin al'aura saboda rashin gudanawar jinin jikinka yadda ya kamata.
2. CIWON SUGAR (DIABETES) idan kana fama dashi shima yana mutukar kashe al'aurar namiji.
3. SHAFAR ALJANI KO SIHIRI : idan kana tare da Aljanar soyayya, ko kuma matarka tana fama da JINNUL ASHIQ (namijin dare, Aljanin soyayya) zaku iya gamuwa da matsaloli kala-kala ta bangaren jima'inku.
4. SHAYE SHAYE: shaye shayen Abubuwan da suke sa maye ko kuma shan kwayoyi masu nauyi ga jikin mutum.
5. RASHIN HUTU : Rashin isashen hutu shima babban jigo ne wajen haddasa matsalolin Rashin gamsar da juna ta fuskar mu'amalar auratayya.
Don haka Malam Liman idan kana fama da wani daga cikin abubuwan nan dana lissafa, dole sai ka nemi Hanyar warware tushen chutar sannan Karfinka zai dawo.
Idan kuma duk babu, kawai dai rashin karfin ne Allah ya jarrabceka dashi, to ka nemi Kwazbara cokali 5, Garin Habbatus Sauda Cokali biyar, Ka hadasu waje guda ka nikasu.
Arika diban garinsu cokali guda ana zubawa cikin Kwan kazar gida, ko na Zabuwa. ana soya maka kamar guda 4 kana ci kullum. insha Allah karfinka zai dawo fiye da da.
Kuma ka rika shan kankana sosai. Musamman bayan Magriba ko bayan isha'i.
Da fatan Allah ya sawwake, Allah ya baka lafiya.
WALLAHU A'ALAM.