Assalamu alaikum malam, Y jama'a? Allah ya biyaka da jannatul firdausi, Amin.
Malam kwanan baya na taba rubutuwa akan matsalar kuraje danake fama dasu, har kace inyi amfani da ararrabi. to malam har yanzu ba dama, naje naga likitan fata nayi test iriiri amma ban dace ba. na gargajiya ma an samo mini fiye da kala goma duk basu yi ba. yanzu wani malami yace min iska ne domin idan na sosa ruwa ke fitowola atafin hannuna da kafafuna, na fuska da jikina da sauki.
Sannan wancen sati naga al'adata amma jinin kalar brown ne kuma duk safe yake zuwa tareda murdawar ciki se ya dauke, bezuwa da rana ko dare. dan Allah malam ina baran addu'a Dan bana samun issashen bacci saboda kai kayi.daga wata baiwar Allah dalibar wannan zaure mai albarka.
JAWABI
********
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Hakika dukkan abinda ya samu bawa, to jarrabawa ce daga Ubangijinsa. kuma akwai falala mai girma wacce bayin Allah suke samu idan sunyi hakuri bisa duk irin jarrabawar da ta samesu.
Kiyi hakuri ki dage da addu'a irin ta Annabi Ayyub (as) "RABBI INNEE MASSANIYADH DHURRU WA ANTA ARHAMUR RAHIMEEN". duk lokacin da kikayi sujjada acikin sallarki.
Sannan ki samu Man Zaitun mai kyau (Extra Virgin Olive oil) tare man Habbatus Sauda 'Dan Misra ko kuma na kampanin Hemani. ki hadasu waje guda ki tofa wadannan addu'o'in acikinsa sannan ki rika shafawa kuma kina sha:
1. FATIHA 7
2. AYATUL KURSIYYI 33
3. LA ILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNEE KUNTU MINAZ ZALIMEEN 11.
4. INNE MASSANIYADH DHURRU WA ANTA ARHAMUR RAHIMEEN 41.
5. QUL HUWALLAHU 33.
6. SURATUL FALAQ DA SURATUN NAAS 33.
7. ALLAHUMMA RABBAN NAAS AZHIBIL BA'AS WASHFI ANTASH SHAAFEE, LA SHIFA'A ILLA SHIFA'UKA. SHIFA'AN LAA YUGHADHIRU SAQMAN (kafa 3).
8. AS'ALUL LAHAL AZEEM RABBAL ARSHIL AZEEM AN YASHFIYANEE (kafa 7).
9. Salatun Nabiyyi (saww) kafa 10.
10. Ayatush shifa'i kafa 7.
Ki tofa aciki sannan ki rabashi gida biyu, ki rika shan rabi. rabi kuma kina shafawa ajikinki. Shi wanda zaki sha din, zaki iya hadawa da zuma kina sha.
Kuma zaki iya tofawa acikin ruwan zamzam ko ordinary water ki mayar dashi shine ruwan shanki ko yaushe.
INSHA ALLAHU ko ma wacce irin chuta ce ajikin mutum yake fama da ita, in dai yayi amfani da wannan addu'o'in da aka tofa, to zai samu lafiya da izinin Allah. mutukar dai yayi imani da Allah da Manzonsa, kuma ya yarda cewa Alqur'ani yana magani..
ZAUREN FIQHU yayi izini ga dukkan wanda yaga wannan post din yayi sharing zuwa ga 'yan uwa Musulmai domin su amfana.